Inna Galadima Ta APC Ta Zama Shugabar Karamar Hukama Mace Ta Farko A Jihar Borno

Inna Galadima

Hajiya Inna Galadima ta jam'iyyar APC, ta zama zababbiyar shugabar karamar hukumar Jere ta jihar Borno, ta kasance Shugabar Karamar Hukuma mace ta farko a jihar.

Ba wannan ne karon farko da mace ta zama Shugabar Kamar Hukuma a jihar Borno ba, domin kuwa, kafin zaben ta, Fanta Baba Shehu ta kasance macen farko da ta zama Shugabar Karamar Hukuma a jihar, sai dai, da farko, an zabe ta ne a matsayin mataimakiyar shugaba a karkashin rusasshiyar jam’iyyar United Nigeria Congress Party (UNCP), sannan daga baya, ta gaji kujerar Shugaban Karamar Hukumar bayan ya rasu.

Farfesa Mohammed Konto Jami’in zabe na karamar hukumar Jere, shine ya ayyana Galadima a matsayin wadda ta lashe zaben, bayan da ta samu kuri’u 110,459 inda ta kayar da abokin hamayyarta na jam’iyyar PDP da ya samu kuri’u 2,478.

A lokutan baya, Inna Galadima ta rike matsayin kwamishina, da kuma mai ba da shawara ta musamman ga gwamnatin jihar a lokuta daban-daban.