Ingila Ta Sallami Jamus Daga Gasar Euro 2020

Dan wasan Ingila Harry Kane (Hoto: AP)

Yanzu Ingila za ta hadu da Sweden ko Ukraine, wadanda za su kara nan ba da jimawa ba a birnin Glasgow.

Ingila ta doke Jamus da ci 2-0 a gasar cin kofin nahiyar turai ta 2020.

Raheem Sterling da Harry Kane ne suka ci kwallayen.

Hakan na nufin Ingila ta kai matakin quarter-finals kenan a gasar, wacce tuni an cire Portugal da ke rike da kofin.

Raheem ne ya fara zira kwallonsa a minti na 75 sai ta Kane ta biyo baya a minti na 86.

Kasashen biyu sun kara ne a filin wasa na Wembley, wasan da ya maimaita karawarsu a wasan karshe na gasar cin kofin duniya a 1966 a filin na Wembley.

Wannan shi ne karon farko da Kane ya samu damar zira kwallo tun da aka fara wannan gasa.

Yanzu Ingila za ta hadu da Sweden ko Ukraine, wadanda za su kara nan ba da jimawa ba a birnin Glasgow.