Rahotanni sun bayyana cewa direban nan da akan kama da zargin safarar mutane, dan shekaru 60 da haihuwa mai suna James Bradley Jr. daga Florida, zai iya fuskantar hukuncin daurin rai da rai ko kuma na kisa a cewar jami’ai.
An tsare Bradley ne a San Antonio, a ranar Lahadi bayan 'yan sanda sun gano gawarwakin mutane takwas a bayan babbar mota, cikin tsananin zafi a wajen ajiye motoci na kantin Walmart. Biyu daga cikin wadanda abin ya shafa sun mutu daga baya yayin da sauran aka kaisu asibiti kuma suna cikin mummunan yanayi, bayan zafi da ya illata su. Jami’ai sunce suna fargabar yiwuwar karuwar yawan wadanda zasu mutu sakamakon hadarin.
Kamar yadda kotun aikata manyan laifuka ta bayyana, Bradley, ya bayyana wa jami’an gwamnatin tarayya masu gudanar da bincike cewar ya tuko motar ne daga Schaller, IOWA zuwa Brownsville, Texas kuma bai da masaniyar akwai mutane a cikin motar sai bayan ya tsaya a San Antonio.
Bradley ya bayyana cewar yana bude bayan motar “Mamaki ya kamani saboda ganin Sifaniyawa sun banke ni har sai da na fadi kasa,” kamar yadda takardun kotun suka nuna . Masu bincike sun ce Bradley ya kira matarsa , a maimakon lambar agajin gaggawa ta 911 duk da cewar yasan cewar an rasa rayuka, takardun sun kuma nuna cewar Matar sa bata amsa wayar ba.
Wadanda suka ganewa idanunsu sun bayyana cewar anyi smogal din kimanin mutane 100 a bayan motar a yayin tafiyar.