Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Surukin Shugaba Trump Ya Ce Bai Da Wata Haramtacciyar Alaka Da Wata Kasar Waje


Mr. Jared Kushner kenan lokacin da ya iso Majalisar Tarayyar Amurka, Capital Hill.
Mr. Jared Kushner kenan lokacin da ya iso Majalisar Tarayyar Amurka, Capital Hill.

Surukin Shugaba Donald Trump, Jared Kushner, ya ce shi bai da wata haramtacciyar alaka da wata kasar waje. Wannan na faruwa ne a cigaba da binciken da ake yi game da katsalandan din Rasha a zaben Amurba.

Jared Kushner, wanda suruki ne ga Shugaban Amurka Donald Trump kuma mai ba shi shawara na kud-da-kud, ya ce shi bai taba yin wata haramtacciyar hulda ko hada baki da wata gwamnatin kasar waje ba.

Kushner ya fita da takardar bayani yau Litini gabanin gurfanarsa gaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Tsaro, da kuma wacce zai yi gobe Talata gaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Harkokin Tsaron, a cigaba da binciken da su ke yi kan katsalandan din da Rasha ta yi a zaben Amurka na bara.

"Bayanin da na ke gabatarwa zai nuna cewa na hadu da 'yan Rasha watakila sau hudu cikin jerin tarurrukan da na yi da jama'a a dubban lokuta a tsawon lokacin yakin neman zabe, da kuma lokacin shirin mika mulki, kuma babu daya daga cinkinsu da ke da nasaba da zabe ko kuma muhimmanci da har za a iya tunawa sosai," a cewar Kushner.

Ya kuma yi bayani game da wasu takaitattun tattaunwar da ya yi da Jakadan Rasha a Amurka, ya ce sun tattauna muhimmancin inganta huldar Amurka da Rasha, to amma ya karyata rahotannin kafafen yada labarai da ke cewa da shi da Jakada Sergey Kislyak sun yi wasu zantattukan ta wayar tarho.

Wata ganawar da ta hada da wata lauyar kasar Rasha ta ja hankali jama'a sosai, musamman tun bayan da dan Shugaban Kasa Eric Trump, ya bayyana jerin sakonnin email da ke nuna cewa ya nuna sha'awar samun abin da ya yi imanin cewa wasu bayanai ne na tabargazar Clinton da lauya 'yar Rashar za ta ba shi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG