Hajiya Turai ‘Yar Adua tace “gaskiya yanzu iyaye na baiwa yara mata damar yin karatu, ba kamar lokacinmu ba.
A lokacin mu, wadansu daga Firamari sai a cire yarinya ayi mata aure. Sai dai kawai, matsalar itace akwai iyayen da basu da kudi, maimakon su saka yaran a makaranta, sun gwammace su baiwa na miji saboda shine yake kula da gida. To irin wadannan yaran ne idan muka samu, sai mu basu tallafin karatu.”
Idan aka kwatanta karatun yara mata a arewacin Najeriya da kudanci fa? Hajiya Turai cewa tayi:
“Da gaske yaran kudu sunyi wa na arewa fintinkau. Har yanzu a arewa muna da wannan tunani mai cewa yaro na miji yafi yarinya mace. Sai a ce ai mace idan tayi aure, sai tayi a gidan mijinta, sun mance cewa idan ka ilimantar da mace daya, to ka ilimantar da al-umma kennan. Duk yarinyar da kika baiwa ilimi, zata kula da mijinta, zata kula da ‘ya’yanta.
Your browser doesn’t support HTML5