Shugaban Sashen Leo Keyen yayi karin bayani akan dalilin kirkiro wannan shiri.
“Abunda yasa muka kirkiro da wannan shiri, saboda mun san cewa zabe shine tubulin gina domokradiyya. Idan babu zabe mai inganci, zabe tsakani da Allah, zabe wanda za’a zabi irin mutanen da ake so, kuma a jefa kuri’a su ci zabe, a tabbatar da su. To anan ne ake samun tangarda a demokradiyyar duk duniya. Kaga yanzu abunda yasa muka kirkiro wannan shiri, domin duba abunda yake faruwa da zabe a nahiyar Afirka baki daya.
Shugaban yayi karin haske akan yadda ake samun nasarar zabe a kasashen yammacin Afirka.
“Zance ne fa na ilimi, a ilimantar da mutane akan zancen zabe, su san muhimmancin zabe, su san cewa zabe ne za’a yi amfani da shi wajen gina demokradiyya. To idan ba’a yi wannan ba, to wasan yara ake”, inji Shugaban.
Za’a fara watsa shirin Zabe ko Nadi ranar Lahadi ta radiyo da karfe 6 na safe, agogon Najeriya da Janhuriyar Nijar.