Daliban kwalegin horas da malamai ta garin Gombe sunyi wani zanga zangar lumana, a lokacin da Ministan Ilimin kasar Mal. Ibrahim Shekarau, ya kai wata ziyara a kwalegin. A jawabinshi yayi maganar cewar wannan ziyarar da sukeyi duk sati suna duba aiyukan da gwamnati tarayya taba ma ‘yan kwangila ne, ko suna yi yadda yakamata, da kuma tattaunawa da hukumomin makarantun don jin matsalolinsu, kana da daliba.
Amma dai a cikin bayanin nashi bai tabo maganar zanga zangar daliban ba. Su dai daliban sun nuna rashin gamsuwa da yadda gwamnati ke nuna halin ko inkula a fannin ilimi. Inda suke cewar basu da ruwansha balle ma na wanka. Mafi akasarinsu suna amfani da ruwan leda ne su yi wanka ko wani bukatunsu. Sun kuma ce babu kayan karatu da dai sauran abubuwan da yakamata ace dalibai na moremawa.