Babban makasudin taron shi ne fadakar da mutane, musamman matasa, akan tada hankulan jama'a da aikata miyagun laifuka kamar lokacin manyan zabuka irin wadanda Najeriya zata fuskanta.
Abubakar Mukhtar Salisu dake zama daya daga cikin jigajigan wandanda suka shirya taron daga gidauniyar IDN yayi karin haske. Yace kungiyar tayi nazari bisa abubuwa marasa dadi da suke faruwa cikin al'umma. Misali a bi muslmi har masallaci a kasheshi ko kirista a bishi cikin mijami'a a kasheshi babu dadi. Sai suka ga haki ne akansu su bada tasu gudunmawar wajen wayar da kawunan al'umma domin dakile ta'adanci.
Dr Tasiru Namadi Bari wanda ya gabatar da makala akan ma'ana da nau'ikan ta'adanci da kuma abubuwan dake kawoshi a cikin al'umma. Yace abu na farko dake kawo ta'adanci zalunci.Abu na biyu shi ne jahilci. Ilimi haske ne jahilci kuma duhu ne. Abu na uku shi ne talauci ko yunwa. Wadannan sune manyan dalilan dake kawo rashin zaman lafiya cikin al'umma.
Shi kuwa Malam Sammani Salga tsokaci ya yiwa mahalartan taron dangane da tsare-tsaren musulunci na zaman lafiya tare da wadanda ba musulmi ba. Yayin da Annabi Muhammad (S.A.W.) ya je Madina ya kira Yahudawa sun zauna tare an yi tsari ta yadda musulmi ba zai yiwa wanda ba musulmi ba wani abu. Haka ma wanda ba musulmi ba ba zai yiwa musulmi wani abu ba. Dole ne musulmi da wanda ba muslmi ba su zauna su yi yarjejeniya ta yadda ba za'a cuci juna ba. Duk wanda ya karya shirin, to akwai hukunci da za'a yi masa.
Wasu da suka halarci taron sun nuna gamsuwarsu da abubuwan da suka koya.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.