Sarkin Kano Mai Martaba Muhammad Lamido Sanusi II yace kabilar Fulani tana da halaye da dabi'u da take alfahari dasu.
Yayi fatan kungiyar Fulani zata tabbatar da horas da 'ya'yanta akan halayen Fulani da dab'iunsu. Ban da haka yace su yadasu a cikin sauran kabilun kasar. Ya gargadesu su cigaba da riko da jaddada addini.
Sabili da irin ayyukan da su Shehu Dan Fodio su kayi bai kamata a ce su da suka rage sun bar aikin ba.
Sarki Sanusi II yace akwai abubuwa suna tasowa a kasar na fitintinu da fada tsakanin makiyaya da manoma. Su yi kokari duk inda suke su zauna lafiya. Yace kare kai baya yiwuwa sai da karfin arziki. Ilimi da arziki suna cikin abubuwan da zasu taimaka masu wajen kare martabarsu da mutuncinsu a cikin kasa.
Sarkin ya cigaba da cewa a cigaba wajen taimakawa sha'anin tsaron kasa. Yace kasar na cikin wani hali inda wasu mutane suna ganin ya zama addinisu su afkawa musulmi. Yace irin wannan abun duk da rashin dadinsa bashi da wani magani illa a fuskanceshi ba tare da tsoronsa ba.
Sarki Sanusi II yace idan mutane sun kawo yaki yakarsu a keyi sai an kaisu kasa. Shiru da rashin magana akansu ko jin tsoronsu ba zai hana su yi abun da su keyi ba. Wannan fitina bata da magani illa a yaki mutanen a kaisu kasa.
Sarkin yace "Mu nan an kawo mana yaki mu ma muna cikin yaki dasu". Ya kara da cewa kamata yayi duk musulmai su san cewa "yakin nan gaba daya aka kawo mana". Yace a taimaka a hada kai da jami'an tsaro a yi yakin. Idan ba haka ba ba za'a yi maganin fitinar ba.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5