Wannan al'amari ya bayyana karara irin tasirin jerin takunkuman da manyan kasashen duniya da kungiyoyin ksaa-da-kasa suka kakaba wa kasar ta Nijar, sakamakon juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023. Sai dai wasu ‘yan kasar na ganin akwai gyara ga wannan tsari.
Sanarwar da hukumomin CNSP suka bayar ta ce za'a yi amfani da kudaden wannan gidauniya ta fonds de solidarite a wani bangare na ayukan horar da jami’an tsaron da ke yaki da ‘yan ta’adda. Haka kuma za dauki dawainiyar ‘yan gudun hijirar cikin gida a sansanoninsu har zuwa lokacin mayar da su gida ta hanyar wannan gidauniya.
Wani dan siyasa Habibou Kane Kadaoure yace matakin gwamnatin abin yabawa ne.
Za'a sami kudaden gidauniyar ne ta hanyar zaftare wani kaso daga kudaden man fetur da wani kason da za'a fitar daga harajin da kamfanonin waya ke zuba wa a hukumar kula da wannan fanni inji sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa za'a rika cire dala biyu wato tamma 10 na cfa a kowane tikitin shiga motocin haya, yayin da kuma za'a zaftare jaka 1 daga kudaden tikitin jirgin sama, kamar yadda za'a fara zaftare dala 2 a kowane kira na wayar telephone da izinin mai kira.
Sai dai wani dan kasar Abba Habibou na ganin tsarin na bukatar gyara, la’akari da yadda tasirin takunkumin kungiyar CEDEAO ya bayyana a fili a galibin harakokin jama’ar Nijer na yau da kullum.
Hakan ya sa wani dan siyasa Chayib Mohamed yake mamakin matakin kafa wannan gidauniya a dai dai lokacin da ‘yan kasa suke cikin mawuyacin hali.
Kashi 40 daga cikin 100 na kasafin kudin shekara abu ne da ke shiga aljihun gwamnatin Nijer daga tallafin kasashe aminnai da kungiyoyin kasa-da-kasa.
Ganin yadda abokan hulda suka janye jiki bayan kifar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum ya sa a farkon makon jiya majalissar soja ta CNSP da gwamnatin rikon kwarya suka yanke shawarar zaftare billion 1000 na cfa daga kasafin kudin shekarar 2023, matakin da kai tsaye ke zama silar soke wasu aiyuka da dama.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5