NIAMEY, NIGER - To sai dai kungiyoyin kare hakkin mabukata na gargadi ga mahukunta akan bukatar karfafa hanyoyin daidaita farashin kayayaki don ganin talakka ya ga zahiri a kasa.
Lura da yadda farashin kayayaki da dama ya yi tashin gwauron zabi a Nijar bayan karin kudin man dizel ya sa gwamnatin kasar kafa wani kwamitin ministoci domin tunkarar wannan al’amari da ya jefa talakawa cikin halin kangi.
Gwamnatin ta ce za ta ci gaba da tattaunawa da dukkan masu hannu a harakokin saye da sayarwa don duba hanyoyin sauke wani bangare na abubuwan da ke janyo tsawwala farashin kayaki.
Shugaban kungiyar ADDC WADATA mai kare hakkin mabukata wato Malan Maman Nouri ya shawarci hukumomi su dubi albashin ma’akaita kamar yadda ya zama wajibi su dauki matakin bin diddigi don tantance farashin kaya a kasuwanni.
A nan ministan makamashi ya ce kwamitinsa ya tanadi hanyoyin daidaita farashi don tabbatar da cewa ‘yan kasuwa da masu sufuri ba su saba alkawari ba.
Gwamnatin ta Nijar, ta hanyar kwamitin ministoci mai kula da yaki da tsadar rayuwa, ta ce ta kara tsaurara matakan tsaro akan iyakoki don farautar masu sarande man gaz oil zuwa ketare kamar yadda a cikin daren Litinin wayewar jiya Talata jami’an tsaro suka kama wasu motocin dakon mai a Gaya dauke da lita 64000 na man diezel lokacin da suke kokarin tasallakawa Jamhuriyar Benin.
Saurari rahoton Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5