Hukumomin Jihar FIlato Sun Bayyana Damuwarsu Game Da Zubar Da Shara Barkatai A Garin Jos 

Hukumomin Jihar FIlato Sun Bayyana Damuwarsu Game Da Zubar Da Shara A Garin Jos.

Hukumomi a karamar hukumar Jos ta Arewa sun bayyana damuwarsu kan yadda jama’a ke zubar da shara barkatai a cikin gari.

PLATEAU, NIGERIA - Shara babban mataki ne na tsabta amma zubadda shi ba bisa ka’ida ba, yakan iya zama cuta ga al’umma.

Hukumomin Jihar FIlato Sun Bayyana Damuwarsu Game Da Zubadda Shara A Garin Jos

Shugaban karamar hukumar Jos ta Arewa Shehu Bala Usman ya ce gwamnati zata yi dirar mikiya kan wadanda ke zubar da shara barkatai, kamar yadda yanzu shara take a ko ina cikin garin.

Yusuf Tanko wani mazaunin garin Jos ya ce dole sai hukumomi sun tashi tsaye wajen hana zubar da shara a koina, domin abin ya yi yawa.

Hukumomin Jihar FIlato Sun Bayyana Damuwarsu Game Da Zubadda Shara A Garin Jos

Hukumomin Jihar FIlato Sun Bayyana Damuwarsu Game Da Zubadda Shara A Garin Jos

Wata mace da ta bukaci mu boye sunanta, tace su dai a unguwarsu sun dauki matakai masu tsari na zubar da shara.

Jami’ar dake wayar da kan jama’a kan kiwon lafiya a karamar hukumar Jos ta Arewa, Hajiya Rakiya Munka’ilu Kantana ta ja hankalin al’umma ne kan cututtuka da zubar da shara ba bisa ka’ida ba, zai iya haifarwa.

Saurari cikakken rahoton daga Zainab Babaji:

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumomin Jihar FIlato Sun Bayyana Damuwarsu Game Da Zubadda Shara A Garin Jos .mp3