Hukumomi Sun Tabbatar Da Mutuwar "Buharin Daji" Na Zamfara

'Yan Bindiga Barayin Shanu A Zamfara

Hukumomi a jihar Zamfara sun tabbatar da mutuwar shugaban Fulani ‘yan bindiga da aka fi sani da Buharin Daji, wanda ke zama jigon rashin zaman lafiya ta hanyar kai hare-hare da satar shanu da kuma garkuwa da mutane a yankin.

Tun a ranar Alhamis din da ta gabata ne ake ta yada jita-jitar labarin an kashe shugaban Fulani ‘yan bindigar jihar Zamfara, wanda ake wa lakabi da Buharin Daji.

Sai dai labarin ya tabbata ne bayan da jami’an soji suka shiga dajin Dan Sadau suka tabbatar tare da dauko gawarsa zuwa Gusau babban birnin jihar.

Da yake bayanin yadda aka kashe Buharin Daji, Nuhu Dan Sadau, dan jarida mai zaman kansa a yankin, ya ce yaran Buharin Daji ne suka je gidan sirikan Dogon Gide suka kashe yara uku tare da daukar dukiya da kuma yin lalata da matan wadanda aka kashen.

Hakan ya sa Dogo Gide ya mamayi Buharin Daji ya bude masa wuta inda ya kashe shi tare da wasu yaransa wajen su 10.

Mai bai wa gwamna shawara kuma daya daga cikin ‘yan kwamitin sulhu da samar da zaman lafiya a jihar Sani Gwamna Mayanci ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Labarin mutuwar Buharin Daji dai ta farantawa mutane da yawa a fadin jihar.

A cewar wasu mazauna yankin da Muryar Amurka ta zanta da su, mutane sun taro garin Dan Sadau domin murnar wannan lamari da ya faru.

Shekarar da ta gabata ne gwamnatin jihar Zamfara ta gudanar da wani shirin sulhu da ‘yan bindigar karkashin jagorancin Buharin Daji, wanda daga bisani shirin ya wargaje inda ‘yan bindigar suka koma kai hare-hare da satar shanu.

Domin karin bayani saurari cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Murtala Faruk Sanyinna.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumomi Sun Tabbatar Da Mutuwar "Buharin Daji" Na Zamfara- 3'00"