Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Mata Ta Duniya; 'Yan Majalisar Dokokin Amurka Mata Sun Ja Hankali Kan illar Boko Haram


Yar majalisa Fredrica Wilson da wadansu 'yan majalisa tare da yammatan Bama
Yar majalisa Fredrica Wilson da wadansu 'yan majalisa tare da yammatan Bama

Yayinda kungiyoyin mata da ‘yan gwaggwarmaqya suka kara yi amfani da ranar mata ta duniya wajen jan hankalin al’umma kan kabubalai da mata ke fuskanta,

A nan Amurka, ‘yan majalisar dokokin kasa mata karkashin jarogancin ‘yar majalisar wakilai mai wakiltar jihar Florida sun yi wani zaman tattaunawa na musamman domin nazari da musayar miyau kan ci gaba ko akasin haka da aka samu a yaki da kungiyar Boko Haram a Najeriya, kungiyar dake da alhakin sace daruruwan mutane da suka hada da mata da kananan yara, da ya hada da sace ‘yammata a makarantunsu na kwana, da ya hada da na baya bayan nan da suka sace yammata dari da goma a makarantar sakandare ta Dapchi, baya ga yammata dari biyu da saba’in da shida da suka sace kimanin shekaru hudu da suka shige a garin Chibok, da har yanzu suke rike da ‘yammata dari da goma sha biyu.

Sai dai tun kafin sace ‘yammatan sakandaren Chibok da ya jawo hankalin kasashen duniya, kungiyar ta sace ‘yammata da dama a arewa maso gabashin kasar inda take tada kayar baya da suka hada da yammata da dama da kungiyar ta sace a garin Bama.

A wannan zaman tattaunawar na musamman, yan majalisar sun karbi bakuncin wadansu ‘yammata biyu daga da zamu saya sunayensu bisa dalilan tsaro da kungiyar ta sace ta kuma kuma aure su da karfi da yaji, banda haka kuma wadansu mayaka da dama suka rika yi masu fyade ba dare ba rana.

A cikin dogon bayanin wahalar da suka sha a hannun kungiyar Boko Haram, daya daga cikin ‘yammatan wadda aka sace ta tana da shekaru goma sha hudu ta bayyana irin akuba da mayakan suka gasa maku lokacin da suka fara yunkurin guda bayanda mayakan sufa fita kai hare hare.

Yammatan sun kuma yi kira da a taimakawa sauran wadanda kungiyar ta sace a kuma basu damar karatu kamar yadda suka samu tare da tallafin wata kungiya dake yaki da aurar da ‘yaya mata suna kanana da ake kira ‘Too young to wed”

A nata bayanin, shugabar kungiyar Stephanie Sinclair, wadda ta sami lambar yabo ta Pulitzer da ake ba matan da suka yi fice a aikin jarida ta bayyana cewa aikin da take yi a wuraren da ake tashin hankali ya bude mata ido ta ga irin yadda tashin hankali ke jefa iyali musamma ‘yammata cikin halin kunci wadanda da dama ake yiwa fyade a yi masu auren dole a kuma tauye masu hakinsu na zuwa makaranta.

“Na shafe shekaru ishirin yanzu ina rubuta kalubalai da kananan yara mata suke fuskanta a kasashen duniya a wuraren da ake tashin hankali inda nake da kwarewa, ina da kwarewa kan abinda ya shafi aurar da yara suna kanana, na hakikanta cewa, idan muka daga yawan shekarun da za a iya aurar da yara, zamu iya samu a inganta rayuwarsu har su iya tafiya makaranta har da zasu iya kula da kansu su kuma zama da taimako ga al’umma.”

Jagorar wannan taron ‘yar majalisar Frederica Wilson, ta bayyana cewa, kamfen da take jagoranta a majalisar dokokin Amurka ta yin tsayin daka sai an dawo da yammatan da aka sace, kamfe ne na neman a saki dukan wadanda kungiyar Boko Haram ke rike da su ba ‘yammatan Chibok kadai ba.

Tace lokacin da muka je Najeriya muka dawo da sakon nan a dawo mana da ‘yanmatanmu, haka kuma dukan lokutan nan uku da muka je najeriya, abinda muke jadadawa shine wannan kiran a dawo mana da dukan yammatan da aka sace a Najeriya, mun sani akwai yammata da yawa da aka sace banda yammatan Chibok, sai dai ‘yammatan Chibok sun zama tambari ne na irin yadda kungiyar take cin karenta ba babbaka a Najeriya da kuma tauye hakin al’umma. Yanzu kuma da aka kara sace wadansu yammata dari da goma ko ma fin haka, zamu sake kara jadada kiranmu ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kara azama na shawo kan wannan kungiyar.

‘Yan majalisa mata da suka halarci wannan zaman sun yi jawabai tare da kara jadada niyarsu ta jajircewa wajen ganin gwamnatin Amurka kara kudin da take kashewa wajen tallafawa ayyukan jinkai a kasashen waje domin wadanda suke fuskantar kalubalar rayuwa kamar yammatan da kungiyar Boko Haram ta sace, da kuma ‘yan gudun hijira na cikin gida zasu iya samun tallafi.

Yan majalisar dokokin Amurka mata sun tattauna kan illar Boko Haram
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:19 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG