Koda yake ba shine karon farko da harin ta’addanci ke rutsawa da jama’a a wuraren ibada ba, a wannan lokaci na tabarbarewar al’amuran tsaro, harin na masallatan kasar New Zeland wani abu ne da ake kallonsa tamkar wani abin ba za ta.
A cikin hirarsa da Sashen Hausa, Reverend Sabo Batshiri na majami’ar da ake kira EGLISE AD a nan yamai yace ya kamata duk lokacin da aka fuskanci matsala irin wannan a tashi tsaye baki daya ko da wanene ya shafa. Yace akwai bukatar duniya tayi magana da baki daya a tsautawa masu irin wannan aikin da ya ce ko da menene tunanin mai aikata irin wannan tashin hankali, babban laifi ne.
A nashi bayanin, Limamin masallacin majalisar dokokin Nijer Malan Haja Alalo na kallon kisan na masallatan CHRISTCHURCH tamkar wata jarabta mai dauke da abubuwan ishara ga musulmi.
Shugaban kasar Nijer Issouhou Mahamadou dake bayyana ra’ayinsa akan harin na new zeland ya rubuta a shafinsa na tweeter cewa, « ina jajantawa al’umar Nouvelle Zeland da iyallan wadanda wannan al’amari ya rutsa da su » sannan ya ci gaba da cewa, « kisan gillar na Chirstchurch wani abin takaici ne dake kara tunatar da duniya cewa ta’addanci wani abu da ba shi da iyaka wanda kuma da ya kamata a yake shi a kowane mataki. »
Saurari cikakken rahoton Souley Mummuni Barma
Your browser doesn’t support HTML5