Shahararren lauya Mr. Femi Falana yace hukumar zaben INEC bata da ikon gudanar da zabukan a karkashin kundun tsarin milkin kasar kasancewa kwamishanonin zabe dake hedkwatar hukumar guda biyu ne kawai maimakon akalla guda biyar.
Amma hukumar zaben bata yadda da matsayin babban lauyan ba.Nick Dazan yace tun watan shida na wannan shekarar suka fitar da jadawalin zabukan lokacin da suke da kwamishanoni 13.
A cikin kundun tsarin mulki sashen da ya shafi aikin hukumar ya ce idan an sami kwamishana daya cikin uku ana iya gudanar da zabe.
Su ma jam'iyyun kasar sun shirya tsaf domin tunkarar zaben. Maimala Boni sakataren jam'iyyar APC na kasa yace suna da kwarin gwuiwar lashe zabukan saboda mutanen dake jihohin biyu sun kosa da halin da suke ciki yanzu. Suna bukatar canji.
Shi ma gwamnan jihar Kogi Idris Wada ya karfafa magoya bayansa saboda zasu sami nasara.
Mataimakin kakakin jam'iyyar PDP na kasa Barrister Abdullahi Jalo yace da yaddar Allah jihohin biyu zasu cigaba da kasancewa hannun PDP.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5