Hukumar Zabe INEC ta Fitar da Ka'idojin Zaben Cike Gurbin Gwamnan Jihar Adamawa

Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, (INEC) Attahiru Jega

Hukumar zabe INEC tace kafin nan da bakwai ga watan gobe jam'iyyun siyasa su kammala fitar da 'yan takarasu su kuma mika sunayensu kafin sha bakwai ga watan goben. Kowace jam'iyya zata kai Abuja sanarwar tantance dan takaranta.

Barrister Kasimu Geidan kwamishanan INEC mai kula da jihar Adamawa shi ya bayyana shirin da hukumar ta INEC tayi domin zaben cike gurbin gwamnan Adamawa biyo bayan tsige gwamnan jihar Murtala Nyako da 'yan majalisar jihar suka yi.

Batun zaben cike gurbin dai ya jawo cecekuce a jihar dangane da wanda ya cancanta ta maye gurbin tsohon gwamnan. Yanzu dai 'yan takara goma sha biyar suka fito suna neman kujerar a inuwar jam'iyyar PDP.

Dan takara Dr Umar Ado na zargin cewa shugabannin jam'iyyar a jihar na neman yi masu zagon kasa inda ya bada misali da kyaututukan motoci da tsohon shugaban hukumar EFCC Nuhu Ribadu da wasu 'yan takara suka baiwa jam'iyyar a jihar. Yace biri yayi kama da mutum. Wadanda da suna zargin PDP cewa jam'iyyar barayi ce yau sun dawo suna fafatawa domin su shiga jam'iyyar. Idan aka yiwa PDP auren dole za'a ji kwaramniya a daki.

Sun kori Nyako domin bai yi abun da yakamata ba. Kuma duk wanda bai yi abun da yakamata ba ya ga abun da baya so.

Magoya bayan Nuhu Ribadu irinsu Alhaji Umar Kalkuleti na ganin tsoron karo da maza ne ke sa wasu kokawa. Yace yanzu shugabannin jam'iyyar sun gane barin mutane kara zube suna cin zabe da sunanta ba tare da yin aikinta ba ya sa suka ga yafi su samu mutane tsarkakku irinsu Nuhu Ribadu. A nemi alfarmarsu su dawo cikin PDP domin suna da shaidar cewa ba zasu yi almundahana ba.

Batun tsayawar mukaddashin gwamnan Ahmed Umaru Fintiri shi ma yana jawo cecekuce. Tsohon mai ba shugaban kasa shawar ta fannin siyasa Ahmed Gulag yace tsayawar Fintiri haramun ne. Idan haka ne wato 'yan majalisa kodayaushe suke son gwamnati sai su tsige gwamna da mataimakinsa su dauki gwamnati. Kundun tsarin milkin kasar bai tanadi hakan ba. Bai kamata a bar Fintiri ya tsaya takara ba. Yana da kujerarsa ta kakakin majalisa wadda sabili da ita ya zama mukaddashin gwamnan. Kundun tsarin mulki ya tanadi cewa idan ya gama aikinsa na wucin gadi zai koma kan kujerarsa ta kakakin majalisa.

Amma magoya bayan Fintiri kamar Stephen Maduwa yace mukaddashin gwamnan dan Najeriya ne kuma dan Adamawa ne sabili da haka yana da 'yancin ya tsaya. A tafiyar Adamawa yau idan yace ba zai tsaya ba talakawa zasu tilasta masa.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Zabe INEC ta Fitar da Ka'idojin Zaben Cika Gurbin Gwamnan Jihar Adamawa - 3'21"