Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abuja Ta Cika da Jama'a Masu Kama Kafa Albarkacin Zaben Badi


PDP
PDP

Zaben shekarar 2015 dake kara karatowa ya sa Abuja ta cika da jama'a masu kame-kamen kafa walau ko suna neman gwamnan jihohinsu ko suna bukatar mukamin minista bayan zabe.

Cikin mutanen da suka cika Abuja har da wadanda suka fi kowa takarkarewa a kafofin labaru domin neman tabbatar da cewa Shugaba Jonathan ya sake tsayawa zabe a shekarar 2015 din.

PDP mai son cigaba da mulki da kuma nufin kwato wasu jihohin adawa na nadawa da rushe wasu shugabanninta na wasu jihohin domin nada wadanda zasu iya ganin jam'iyyar ta sake kafa gwamnatin tarayya, wato ta cigaba da abun da ta soma tun shekarar 1999.

Cikin jihohin da PDP ke hankoron son kwacewa ita ce jihar Yobe, jihar dake cikin dokar ta baci inda ta rushe shugabannin jam'iyyar dake karkashin shugabancin Alhaji Lawal Gana Karasuwa da aka yi amanna na hannun daman Dr Yarima Ngama ne.

Barrister Abdullahi Jalo mataimakin kakakin jam'iyyar na kasa yace APC ce a wajen yakamata a samu mutane masu karfi da zasu saka dukiyarsu cikin jam'iyyar su giriza komi domin a samu gwamnan PDP a Yobe idan Allah ya yadda. Wai mutane sun gaji da adawa a jihar Yobe. Suna son a gwada PDP ko rikicin da ake ciki zai yi sauki.

Daya daga cikin shugabannin da aka rusa Adamu Buni Yani yace matakin da PDP ta dauka gurguwar dabara ce. Yace wadanda suka sa aka yi hakan basu san abun da su keyi ba. Ban da haka shi yana jin tausayin Shugaba Jonathan. Babu yadda za'a ce wanda ya rike garinsu shekara uku sauran wata uku a yi zabe a ce ba za'a samu matsala ba. Wadanda su kayi hakan Jonathan su ke yaka ba son PDP su keyi ba. Idan kuma ya ganosu ya gyara to shi ke nan. Idan za'a yi zabe sau dari mutanen Dr Yarima ne zasu dawo. Yanzu zamanin Dr Yarima ne daga Allah.

PDP na buga kirji ta karfafa dimokradiya bayan janyewar sojoji. Gwamnan Katsina Ibrahim Shema yace dama sai an yi kurakurai kana a cigaba. Amurka ma haka ta taso. Tun 1960 ba'a taba yin gwamnatin dimokradiya ba da ta dore sai wannan karon.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG