Cikin wadanda suka kasance a zauren akwai wakilin jam'iyyar PDP Barrister Bashir Maidugu.
Barrister Maidugu yace akwai kurakurai a dokar kamar zabe bayan zabe wadda dokar ta bada kwana bakwai. A ganinsa da jam'iyyarsa lokacin da doka ta tanada yayi kadan. Yace akwai wasu wuraren da yawa da suka bayar da suna son a yi gyara a kansu.
Akan zargin da ake yiwa PDP cewa tana anfani da karfin iko da take dashi wajen yin abubuwa yadda suka so ba tare da bin doka ba sai Barrister Maidugu yace idan an yi la'akari da shekaru hudu da suka wuce an yi zabuka wadanda mutanen kasar da ma na waje suka yaba. An yabawa hukumar zabe an kuma yabawa gwamnati. PDP bata anfani da wani karfi. Zargin 'yan hamayya ne kawai.
Dr Yunusa Tanko na jam'iyyar gwagwarmaya ta NCP yace gyaran dokar zaben ya zama wajibi idan har ana son a karfafa dimokradiya a kasar da yanzu take cikin shekarunta na goma sha biyar. Yace sun fito da korafe-korafe da suke dashi. Na farko ita ce maganar canza sheka. Bayan mutum yaci zabe a karkashin wata jam'iyya sai kuma ya koma wata. Su basu yadda da hakan ba. Na biyu suna korafi akan kudade da ake hana jam'iyyu.
Su kuma 'yan majalisar dattawa akwai abun da basa so a dokar zaben kasar. Sanata Kabiru Ibrahim Gaya yace akwai abubuwan da suka duba yakamata a gyara. Suna da damuwa akan shirin yin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya rana daya kana na gwamnoni da 'yan majalisun dokokin jihohi rana daya. Idan aka zabi shigaban kasa ba'a zabi gwamnoni ba to za'a samu matsala wajen zaben gwamnonin.
Dan majalisar wakilai Aliyu Gebi ya kalli batun gyaran dokar zabe ta wani fanni ne daban. Duk batun gyaran dokar zabe a ajiyeshi a gefe daya a ceto jama'a. Idan babu jama'a yaya za'a yi zaben. Yau a arewa musamman yankin arewa maso gabas wanene zai fito yayi kemfen. Idan mutane basu fito ba wane zabe za'a yi. Batun yiwa dokar zabe kwaskwarima magana ce ta son rai. Kowa na neman hurumin yadda zai dawo da sassauci da sauransu.
Ga rahoton Medina Dauda.