Hukumar Ya’ki Da Cin Hanci Ta EFCC Ta Kama Shugaban Gidan Radiyon Muryar Nijeriya

EFCC

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa-EFCC, ta damke Shugaban gidan radiyon Muryar Nijeriya Mr. Okechuku Osita da zargin badakala da cin hanci da yakai Naira miliyan dubu’daya da miliyan ‘dari biyu ta aringizon kwangiloli da baiwa ‘yan uwansa ayyukkan boge.

A wata hira ta musamman da Muryar Amurka Abdulrasheed Bawa shugaban EFCC ya ce ba zai iya magana da yawa akan abinda ake tuhumar shugaban ba domin suna kokarin yin bincike kan zargin da kuma tabbatar da cewa sun samu shaidu.

Amma shugaban na EFCC ya ce sun bada wasu ka’idoji da Mr. Ostia ake bukatar ya cika domin samun beli. Ya kuma ce yana yiwuwa Mr. Ostia ya samu beli, kafin zuwa kotu.

Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa (Instagram/EFCC)

Da yake tsokaci dangane da batun, Awwal Musa Rafsanjani shugaban kungiya mai fafutukar yaki da cin hanci da rashawa ya ce ba yau aka fara haka ba, inda jami’ai na gwamnatin iri-iri ba sa bin ka’idojin da dokar da sharruda kan kwangila kuma ya ce shugaban kasa da kansa yaki yin tsayin daka ya tabbatar da cewa an aiwatar da dokar da tsarin ta.

Saurari hirar su cikin sauti daga Umar Farouk Musa:

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Ya’ki Da Cin Hanci Ta EFCC Ta Kama Shugaban Gidan Radiyon Muryar Nijeriya