KADUNA, NIGERIA - Hukumar wanzar da zaman lafiyar, wadda ta kira wani taron masu ruwa da tsaki, ta ce ta na sane da yankunan da ke fama da matsalolin tsaro a sassan Jihar Kaduna amma kuma ta na daukar matakan magance su.
Shugaban hukumar, Dr. Saleh Momale shi ya yi wa manema labarai bayani game da wannan taro. Momale ya ce manyan ayyukan da ke gaban hukumar sune zaben shekarar 2023 da kuma kidaya; saboda akwai bukatar zaman lafiya don gudanar da wadannan ayyuka biyu.
Malam Suleiman Abdul'Aziz wakilin masu bukata ta musamman a hukumar wanzar da zaman lafiyan ta Jihar Kaduna, ya ce hukumar za ta kira dukkan 'yan takara don su sanya hannu kan yarjejeniyar zabe cikin lumana a fadin Jihar baki daya.
Cikin kwanakin nan dai gwamnatin Kaduna ta ce jami'an tsaro na nasara a kan 'yan-bindigan da ke daji har ma ta ceto wasu mutane.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna, Malam Samuel Aruwan ya ce yanzu ayyuka na masamman jami'an tsaro ke yi a dazuzzuka kuma su na samun nasarori.
Hare-haren 'yan-bindiga har sun ma tashi garuruwa da dama a kananan hukumomin Birnin Gwari, Igabi, Chukun, Zangon Kataf da Giwa, sai dai ayyukan jami'an tsaro na baya-bayan nan sun soma samar da natsuwa a zukatan wasu al'ummar wadannan yankunan.
Saurari cikakken rahoton daga Isah Lawal Ikara:
Your browser doesn’t support HTML5