Hukumar NDLEA Ta Kama Wani Da Miyagun Kwayoyi Tan 7.6 Na Sayar Wa ‘Yan Ta’adda

NDLEA ta kama dillalan miyagun kwayoyi

Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya wato NDLEA sun kama wani mutum mai shekaru 42 da aka ce yana jigilar dubunnan miyagun kwayoyin na Opiod a boye zuwa wani yanki na ‘yan tada kayar baya a yankin Banki na jihar Borno.

WASHINGTON, D. C. - Wanda ake zargin dai yana cikin mutane 24 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi a fadin kasar, a cewar kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata.

Miyagun Kwayoyi Da Hukumar NDLEA Ta Kama

Sanarwar ta ce a samamen da aka yi sun kai ga kama wasu miyagun kwayoyi daban-daban da ya kai kilogiram 7,609 a jihohi takwas.

Haka kuma an kama wata mace mai cikin wata shida, mahaifiyar ‘ya’ya uku, da kuma wasu mata uku a cikin wasu manyan samamen.

A cewar sanarwar, an kama mafi yawan masu jigilar kwayoyin ne a jihar Nasarawa inda jami’an hukumar NDLEA da ke aiki bisa sahihan bayanan sirri a ranar Lahadi, 4 ga watan Fabrairu, suka kama wata mota da lambar Legas JJJ 64 YC dauke da buhunan tabar wiwi guda 367 mai nauyin kilogiram 4,037 daga Akure, babban birnin jihar Ondo, wanda za a kai a yankin Shabu da ke Lafia, babban birnin jihar.

Wadanda aka damke ake kuma zargi da hannu a ciki sun hada da Shuaibu Yahaya Liman mai shekaru 35; Litinin Audu, 33; da kuma Linus Samuel mai shekaru 42.

A Abuja kuma jami’an NDLEA sun kama wasu biyu, Jibrin Shuaibu mai shekaru 23 da Prosper Innih mai shekaru 17 a ranar Litinin 5 ga watan Fabrairu.

NDLEA ta kama dillalen miyagun kwayoyi

An kama wadanda ake zargin dauke da jakunkuna 169 da kuma kunshi-kunshi 80 na tabar wiwi mai nauyin kilogiram 1,961.5 da aka boye a cikin wata mota mai lamba ta Ogun WDE 557 XC.