Dubban jama’a ne dai rikicin Boko Haram da aka shafe fiye da shekaru shida ana fama da shi,ya shafa,musamman a jihohin Adamawa,Borno da kuma jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya.
Wannan ne dai karon farko da hukumar ta kwastam ke raba wadannan kayakin tallafin da kanta a jihar Adamawa,daya daga cikin jihohin da rikicin Boko Haram ya shafa.
Kayakin sun hada da abinci,sutura da kuma sabulai,inda aka rabawa al’ummomin da rikicin Boko Haram ya shafa a kananan hukumomi bakwai da a baya suka fada hannun yan bindiga masu tada kayar bayan na Boko Haram,dama sansanonin yan gudun hijira dake jihar Adamawa.
Iya Abubakar shi ne mataimakin shugaban hukumar ta kwastam ,da ya wakilici shugaban hukumar,yace wadannan kayaki na ko cikin kayakin da hukumar ta kame,don haka ta kawo a rabawa wadanda rikicin ya shafa.
Shiko Hon. Musa Ahmad Bello shugaban karamar hukumar Mubi ta Arewa,daya daga cikin yankunan da suka fada hannun yan Boko Haram,yace zasu yi adalci a rabon kayakin.
Suma dai shugabanin kungiyoyin addinin Musulunci da Kirista,sun gargadi jama’a da su yi gaskiya ayayin rabon kayakin tallafin.
Kimanin buhunan shinkafa 5,460 da sabulun wanka katon 78 da jarakunan man girki 600 ne hukumar kwastan din ta kawo domin rabawa al’ummomin da rikicin Boko Haram din ya shafa.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5