Wannan korafin na zuwa ne bayan sama dawatanni biyu da gwamna Sanata Muhammadu Umaru Jibirilla Bindow ya kaddamar da shirin wanda kawo yanzu mutane kasa da dari biyu daga cikin dubu ashirin da takwas suka anfana da taki buhu shida-shida sabanin abinda shirin ya tanada.
Shugaban kungiyar manoman shinkafa ta Najeriya reshen jiha kuma mamba na kwamitin rabon rancen Alhaji. Maikano ya ce an dauki shirin da hannun hagu ta hanyar kyale siyasa shiga cikin al’amarin musamman ta bangaren ‘yan majalisar dokokin jiha dalili ma da ya sa shirin ya gamu da tangarda.
Da yake kare matsayin ‘yan majalisar dokokin jihar Adamawa Hon. Hassan Burguma ya wanke takwarorinsa cewa ba a taba kawo batun shirin rancen noma na Anchor Borrowers Scheme gaban majaklisar ba.
Wata ayar tambaya inji ta bakin wasu manoma irin su Mal. Bukar Jimeta ita ce rashin fayyace masu dalilan da suka sanya kwamitin da kwamishinan ma’aikatar noma ke wa jagoranci rage adadin kadada da kudi da kowane manomi ya kamata ya anfana da shi ba.
Kwamishina ma’aikatar noma na jihar Adamawa Alh. Ahmed Waziri ya fadawa Muryar Amurka sun dauki matakin a matsayin na gwaji ganin damina ta kure kuma da niyyar tallafawa masu noman rani.
Ga rahoton Hassan Adamu da karin bayani
.