kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun dade suna zargin sojojin Nigeria da ‘yan sanda da cewa suna cin zarafin yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu, ciki harda yi musu fyade.
A martanin da ta maida hukumar kai dauki ta Najeriya, NEMA da ita ke kula da sansanonin yan gudun hijira a kasar ta bakin jami’in yada labaranta, Sani Datti, tace akwai abin dubawa game da wannan rahoto.
Sani Datti, yace “A gaskiya mun karanta wannan rahoto, to amma mun yi mamaki, da kuma jimami da nuna bacin ranmu.To amma abin sani shine cewa yadda ake kula da sansanoni, ba hukuma guda ko kungiya guda daya ne ke aiki ko kula da harkokin yan gudun hijira ba, wannan kuma ya fada ne a fannin kariya da kula da walwalar yan hijira dake da fannoni kusan 40.” Ya kuma ce za a gudanar da bincike da kuma hukunta duk wanda aka samu da laifi.
Duk dai kokarin da Muryar Amurka tayi domin jin ta bakin wasu yan gudun hijira kan wannan batu hakan bata samu ba domin duk sun ki magana, inda kowa ke cigaba da gudanar da harkokinsa.
To sai dai kuma babban jami’in hukumar NEMA dake kula da sansanonin yan gudun hijira dake jihohin Adamawa da Taraba, Sa’ad Bello, yace su dai a wajensu ba haka zancen yake ba. inda yake cewa “Ai da sai su fada mana ko a wani sansani ne abin ya faru, domin kawo yanzu mu da muke kula da wadannan sansanoni ba mu da labari.”
Kawo yanzu ma,tuni kungiyoyi masu zaman kansu suka fara maida martani game da rahoton ta Human Rights. Kamar Mallam Musa Jika, na kungiyar Amnesty Support Group, wanda ya bukaci da a gudanar da kwakkwarar bincike kan lamarin.
Kamar yadda alkaluma ke nunawa, kawo yanzu tun bayan fara rikicin Boko Haram, fiye da shekaru Shida, Sama da mutane Miliyan Biyu ne suka bar gidajensu sakamakon rikicin kungiyar Boko Haram.
Domin karin bayani.