Irin wannan hanyar cin zarafin matan ya kara nuna halin takaici da 'yan gudun hijiran suke ciki baicin batun rashin wadatar abinci.
Tuni dai shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya bada umurnin binciken gaskiyar rahoton domin daukan matakin da ya dace.
Mai taimakawa shugaba Buhari kan labaru Garba Shehu yayi karin bayani. Yace da rahoton ya kai garesu shugaban kasa ya nuna damuwarsa tare da bacin rai cewa mata da suka fi rauni da suke zaune a sansanin 'yan gudun hijira a ce har ana zaluntarsu, yace gwamnatinsa ba zata lamunta da irin hakan ba.
Shugaba Buhari ya umurci 'yansanda da shugabannin jihohin Adamawa da Borno da Yobe su bincika lamarin su kawo masa rahoto kafin ya san matakin da zai dauka.
Su gwamnonin na arewa maso gabas da suke da 'yan gudun hijira na kokarin maidasu garuruwansu ko kuma wuraren da suka dace domin rufe sansanonin. Da ma can tsohuwar mai kula da 'yan gudun hijira ta Najeriya Hajiya Sani Kangiwa ta dade tana jan hankali kan wannan lamarin.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.