Hukumar Kula Da Jigilar Kaya Daga Teku Zuwa Nijar Ta Shirya Taron Horar Da Masu Dakon Kaya

A Jamhuriyar Nijar Hukumar kula da ayyukan dakon kaya daga tashoshin jiragen ruwa zuwa sassan kasar ta shirya wani taron horo ga masu dakon kaya da ‘yan kasuwar dake shigo da kaya daga waje ta yadda zasu lakanci dubarun da zasu basu damar cin moriyar wannan fanni fiye da yadda abin yake a yanzu.

Lura da yadda masu motocin dakon kaya daga bakin teku zuwa cikin gida Nijer ke gudanar da aiki cikin yanayi irin na kara zube ya sa hukumar CNUT mai kula da sha’anin suhurin kaya ta fara yunkurin fadakar da su hanyoyin da za su ba su damar gudanar da aiki cikin yanayin mutunci har su ci moriyarsa fiye da can baya. Madame Tchima Moustapha it ace babbar darektar CNUT.

A yanzu haka direbobin motocin dakon kaya da masu motocin dake gudanar da wannan aiki na fuskantar barazanar durkushewar harakoki sakamakon gogayyar dake tsakaninsu da takwarorinsu na kasashen waje ba’idin wasu matsalolin da ake fama da su saboda haka shugaban kungiyar masu shigo da motoci daga waje Alhaji Hamadou Boubakrine ke daukar wannan taro da mahimmanci.

Su ma ‘yan kasuwar dake shigo da kaya daga waje na da babbar damuwa a game da halin da harakokin dakon kaya ke ciki a yau daga bakin teku zuwa Nijer saboda yadda abin ke zama wani bangare na dalilan tsadar kaya a kasuwannin cikin gida inji Chaibou Tchombiano sakataren kungiyar ‘yan kasuwar Import Export.

Masana sha’anin jigilar kayan kasa da kasa ne hukumar ta CNUT ta gayyato domin su bajewa mahalarta wannan taro mahimman ka’idodin aiki da zummar fitar da su daga duhun kan dake dabaibaye tafiyar al’amura a wannan fanni.

A ranar juma’ar dake tafe ake kammala wannan taro da wasu shawarwarin da zasu taimakawa masu motocin dakon kaya da ‘yan kasuwar dake shigo da kaya daga bakin teku wajen gudanar da harakokin yau da kullum.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Kula Da Jigilar Kaya Daga Teku Zuwa Nijer Ta Shirya Taron Horon Masu Dakon Kaya