Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kasuwa Sun Rufe Shaguna a Birnin Yamai, Nijer


NIJER: Yajin aikin 'yan kasuwa
NIJER: Yajin aikin 'yan kasuwa

‘Yan kasuwa sun rufe shagunan ranar Laraba a birnin Yamai da nufin nuna kin amincewa da sabon tsarin karbar kudaden harajin da suke dauka a matsayin babbar barazana ga sha’anin kasuwanci a wannan lokaci da ake fama da matsin tattalin arziki.

Watanni a kalla uku aka shafe ana tattaunawa a tsakanin hukumomi da shugabannin kungiyoyin ‘yan kasa domin neman bakin zaren rikicin da ya barke bayan da gwamnatin Nijer ta bayyana shirin soma zartar da wannan sabon tsari mai amfani da wata na’urar tantance kudaden harajin da suka rataya a wuyan ‘yan kasuwa masu babban jari.

Sai dai har zuwa ranar Talata ba a cimma daidaito ba, mafari kenan da kungiyoyin ‘yan kasuwa suka umurci magoya bayansu su rufe shaguna a wunin ranar Laraba a birnin Yamai.

Alhaji sani Chekarao, shi ne shugaban kungiyar ‘yan kasuwar da ke shigo da kaya daga waje, ya ce wata uku kenen da ba a cimma matsaya ba shi ya sa suka umurci 'yan uwansu 'yan kasuwa su rufe kasunwanci har sai an yi sulhu.

A zagayen da Muryar Amurka ta yi a wasu daga cikin kasuwannin birnin Yamai irin su Petit Marche, da Grand Marche da kasuwar wadata, akasarin shaguna na rufe. Ko da yake a kewayen wadannan kasuwanni masu saide saide sun shanya kayayyaki kuma haka abin yake a kewayen kasuwar Katako, lamarin da ya haddasa damuwa a wajen mutanen da suka je sayayya.

Wani wanda ya yi watsi da umurnin na kungiyoyin ‘yan kasuwa ya bayyana mana dalilansa na bude shago a ranar. Ya na mai cewa su kananan 'yan kasuwa dole sai sun yi kasuwanci kafin su samu kudin ciyar da iyalansu.

A yammacin ranar Laraba Firai Minista Ouhoumoudou Mahamadou zai gana da shugabannin manyan ‘yan kasuwa domin tattauna hanyoyin sassauta farashin ababen masarufi bayan la’akari da yadda farashin irin wadanan kayayaki ya cira sama a wani lokaci da ake shirye shiryen azumin Ramadan, yayin da ake ganin yiyuwar taron ya tabo matsalolin da ‘yan kasuwa ke nuna damuwa akansu.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

XS
SM
MD
LG