Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Fararen Hula Na Tantauna Hanyoyin Samar Da Makamashin Zamani


Kungiyar CODDAE da hadin guiwar Cibiyar bunkasa ayyukan samar da makamashi a nahiyar Afrika (CESAO -AI ) sun shirya taro da nufin tattaro shawarwarin shugabanin kungiyoyin kare hakkin jama’a a fannin makamashi.

Wannan na zuwa ne a wani lokaci da kasashen Afrika ke neman hanyoyin maye guraben injinan samar da makamashi da tashoshin dake amfani da hasken rana a matsayin wani bangare na matakan takaita illolin dumamar yanayi.

Samar da wadatar makamashi kuma akan farashi mai sauki da a dai bangare karfafa matakan kare muhalli daga illolin da canjin yanayi ya haddasa wa duniya a yau buri ne da a shekarun bayan nan kasashen Afrika suka kudiri aniyar cimma don samar da ci gaba mai dorewa mafarin wannan taro na musayar miyau a tsakanin kwararru a fannin makamashi da jami’an kare hakkin jama’a don duba ta inda za a bullo wa wannan yunkuri.

Kwararren akan sha’anin makamashin zamani Pr Albert Wright na daga cikin wadanda suka shirya wannan haduwa. Yace makamashin zamani wani abu ne da ke da matukar mahimmanci wajen yaki da talauci a karkara wanda kuma ke taimaka wa a samu ci gaba mai dorewa sannan hanya ce ta samar da wuta cikin tsafta wanda kuma a kan iya samunta dare da rana.

Amfani da makamashin zamani wata hanya ce ta samar da aikin yi ga jama’ar cikin gida, wani alfano na daban game da irin wannan makamashi shine rage karfin tururin dake gurbata muhalli.

Rashin zamanantar da hanyoyin samar da makamashi musamman wutar lantarki wata matsala ce da jam’ian kare hakkin mabukata suka jima suna jan hankulan hukumomi a kanta a Nijer.

A hirar shi da Muryar Amurka, shugaban kungiyar ADDC Wadata Maman Nouri ya bayyana cewa, wannan taro dama ce ta bada shawarwarin da zasu kai ga samun mafita.

Toshon ministan makamashi Alhaji Rabiou Hassan Yari dake cikin wadanda aka gayyato domin bada gudunmuwa ya yi na’am da wannan yunkuri na kasashen Afrika.

Jamhuriyar Nijer mai yawan jama’a million 22 na sayen wutar lantarki daga Najeriya koda yake kasar ta mallaki wasu tashoshin samar da wutar lantarki da injin duk da cewa wani dan kasar ta Nijer Pr Abdoul Moumouni Dioffo ne ya fara gano hanyar samar da wutar lantarki da hasken rana.

Yunkurin gina madatsar ruwa a kauyen Kandaji na jihar Tilabery da nufin samar da wuta ya ci tura yau shekaru sama da 40.

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG