Hukumar Kaura Ta Duniya Ta Kwashe Bakin Da Su Ka Makale A Libiya

Irin bakin kasashen Afirka da hukumar kaura ta Majalisar Dinkin Duniya, IOM, ta fara kwashewa daga Sabha kasar Libiya za ta maida su gida.

Hukumar Kaura ta Duniya ta fara kwace baki 'yan kasashen Afirka daga kasar Libiya

Hukumar kula da kaura ta MDD ta ce ta fara kwashe baki ‘yan kasashen Afirka fiye da dubu daya da 200 daga garin Sabha na kasar Libiya, wanda a da tunga ce ta tsohon shugaban kasar Moammar Ghadafi.

Hukumar kula da kaura ta Majalisar Dinkin Duniya ta fada litinin din nan a cikin wata sanarwa cewa bakin sun bar garin a cikin manyan motoci 15 wadanda ake kyautata cewa za su yi kimanin mako daya a hanya kafin su isa kan iyakar Chadi da jamahuriyar Nijer. Daga can za a kai su garin Faya Largeau a arewacin kasar Chadi kafin a kai kowa garin su a nan Chadi ko kuma wata kasar Afirka.

Kimanin rabin bakin ‘yan kasar Chadi ne, sauran kuma ‘yan wasu kasashe ne goma na Afirka.

Hukumar kula da kaura ta MDD ta ce fadan da ake gwabzawa ne ya hana ta kaiwa mazauna garin taimako, wanda sai a karshen watan jiya sojojin hukumomin wucin gadi su ka iya kwace shi.

A halin da ake ciki kuma, dan Mr.Ghadafi mai suna Saadi ya musanta zargin hukumar ‘yan sandan kasa da kasa cewa ya yi amfani da makami wajen razana mutane lokacin da yake shugabantar hukumar kwallon kafar kasar. Ya musanta wannan zargi da kakkausar murya a jiya lahadi, haka kuma ya musanta cewa ya yi almundahana da dukiyar kasar.