Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Shugabancin Wuccin Gadin Libiya na kokarin kwace daukacin Sirte


Jerin motoci dauke da mutanen da ke tserewa daga Sirte
Jerin motoci dauke da mutanen da ke tserewa daga Sirte

Mayakan gwamnatin wuccin gadin Libiya, sun kaddamar da abin

Mayakan gwamnatin wuccin gadin Libiya, sun kaddamar da abin da su ka bayyana da cewa shi ne “samamen karshe,” a kan birnin Sirte, daya daga cikin wurare kalilan das u ka rage a hannun tsohon Shugaba Moammar Gaddafi.

Jama’a na ta ficewa daga wannan gari na bakin gabar teku a lokacin da mayakan gwamnati wuccin gadin ke dannawa cikin unguwannin.

A jiya Litini, dakarun gwamntin wuccin gadin sun kwace wani sansani a ciki da wajen Sirte. Cikin wuraren das u ka kama hard a garin Qasr Abu Hadi, inda aka ce anan ne aka haifi Gaddafi cikin wata bukka irin ta makiyaya a ckin 1942.

Jami’an gwamnatin wuccin gadin Libiya sun sha alwashin sauka, bayan an kwace Sirte an kuma yi shelar nasarar kwace dukkannin kasar. Farayim Ministan wuccin gadi Mahmoud Jibril ya fadi jiya Litini cewa kwace Sirte da Majalisar Shugabancin Wuccin Gadin Libiya za ta yi zai sat a iya iko da dukkan yankunan tekun kasar, da na bisa tudu, da samaniya da ma tasoshin jiragen ruwa.

To amman yadda cewa za a cigaba fafatawa a ‘yan wasu wurare a can yankin hamadar da ke kudu, ciki hard a Bani Walid.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG