Dakarun gwamnatin wuccin gadin Libiya tare da taimakon jiragen yakin NATO sun tsananta kawanyar da su ke wa garin haihuwar Moammar Gaddafi wato Sirte, a sa’ilinda su kuma fararen hula keta yinkurin tserewa daga birnin ta wuraren da ake ta kara tsananta bincike.
Dakarun da ke adawa da Gaddafi sun kutsa ta bayan garin Sirte daga gabas a jiya Litini a sa’ilinda jiragen yakin NATO samfurin jet-jet kuma su ka yi ta jefa bama-bamai kan wuraren da dakarun Gaddafi su ka ja daga har zuwa rana ta uku. NATO tace wuraren da ta ke aunawa sun hada da wurin bayar da umurni da kuma ma’adanar kayan yaki.
Dakarun gwamnatin wuccin gadin da suka fito daga Misrata sun yi ta rarraba kayan abinci da ruwan sha ga iyalan da ke gudun tsira a daidai lokacin da motoci shake da fararen hula da ‘yan kayansu keta ficewa daga birnin. Mayakan na Misrata sun yi ta tantance sunayen ‘yan gudun hijira daga jerin sunayen wadanda ake zargi da goyon bayan Gaddafi. Sun tsare wasu daga cikinsu.
Fararen hula da ke gudun tsira, sun ce mayakan bangarorin biyu sun fi mayar da hankali kan nemar ramuwar gayya. Wasunsu kuma sun bayyana irin famar da ake da karancin abinci, da mai, da ruwan sha da kuma magunguna a birnin Sirte, a daidai lokacin da jami’an asibiti ke gargadin karuwar tabarbarewar kiwon lafiya. Kungiyoyin agaji na kasa da kasa na bukatar shiga birnin.