A sanarwar da wata jami’a a hukumar ta IMF mai suna Antoinette Sayer ta aikawa babban bankin Najeriya CBN, tace matakin na kawo cikas ga hada hadar kasuwancin cikin gida da na waje. Alhaji Kasimu Garba Kurfi shine shugaban kamfanin hada hadar kudi a saka jari na APT a birnin Lagos, wanda ya goyi bayan matakin da IMF din ta dauka, inda yace bayadda za’ayi ace Najeriya ta tsayar da farashin dala kasancewar bata da wadatar dalar.
Wakilin Muryar Amurka Babangida Jibrin, ya tambayi mukaddashin kungiyar masu hada hadar kudaden kasashen waje na Najeriya Alhaji Aminu Gwadabe, ko yaya masu hada hadar kudaden kasashen wajen ke kallon matakin gwamnati da kuma na IMF? Wanda ya bada amsa da cewa shi a ganin shi wannan shawarar bata dace ba, saboda IMF na tambayar Najeriya ne ta karyar da darajar Naira da cewa sai anyi haka ne kasar zata zama dai dai.
Ko a cikin wannan makon sai da gwamnan babban bankin tarayyar Najeriya, ya jaddada cewa gwamnati zata duba wannan tsari, domin tallafawa bankuna da kuma ‘yan kasuwa.
Saurari rahotan Babangida Jibrin.
Your browser doesn’t support HTML5