Kasar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, ita ce tafi kowace kasa fama da barazanar matsananciyar yunwa a kasashe masu tasowa bisa alkaluman da aka duba da suka hada har da matsalar mutuwar yara ‘yan kasa da shekaru biyar. Sannan sai kasashen Chadi da kuma Zambia.
Kididdigar ta gano cewa akwai nasaba tsakanin matsalar yunwa da yake-yake da suka yi fama da su a shekarun baya, da kuma wadanda suke aukuwa a yanzu.
Sannan kididdgra ta nuna cewa a sauran jerin kasashen da ke goman fgarko akwai East Timor, Saliyo da Haiti Madagascar da Afghanistan da Nijar da kuma Yemen, wandandu suma duk suna fusknatr barazanar matsananciyar yunwa.
Dr. Klaus Von Grebmer, mai bincike ne a cibiyar mai lura da sha’anin abinci a duniya, a Berlin, inda daga nan ne aka fitar da wannan rahoto. Kuma a hirar da ya yi da Joe De Capua na sashen Ingilishi na Muryar Amurka ya danganta matsalar da rashin zaman lafiya da wasu kasashe ke fama da su a Afrika.
Yace, “Kasashe biyar cikin takwas na farko daga Afrika ne, kuma cikin wadannan biyar din hudu sun tsinci kansu cikin matsananciyar yunwa saboda yake-yake da a ke yi ko kuma wani abu da ke da nasaba da tashin hankali.”
Dr Klaus ya kara da cewa- “A duk lokacin da aka samu tashin hankali na makamai, manoma, ba za su iya shuka irinsu ba, ko sun shuka ba za a samu daman sayar da sub a, sannan babu damar shigar da kayayyakin da za aikin noma da su, baya ga haka hanyoyin da za a gudanar da kasuwanci duk sukan kasance a rufe. Saoda haka tasirin da yaki ke yi akan haifar da yunwa, babban al’amari ne.”
To sai dai a cewar Dr Klaus idan mahukunta suka himmati, kasashen za su iya saura halin da suka tsinci kansu a ciki.
“Idan masu rike da mukaman siyasa suka maida hankali domin ko a nan Afrika, akwai kasashen da suka yi fama da rikici kuma suka fuskanci wannan matsala da suka da Habasha da Rwanda da Angola, amma kuma daga baya da suka samu zaman lafiya, sai aka maganace matsalar yunwa, na san akwai wuya, amma za a iya yi.”
Ga fasarar rahoton da Sarfilu Hashim ya gabatar