Hukumar ICPC Ta Bukaci ‘Yan Najeriya Su Goyi Bayan Buhari A Yaki Rashawa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a Lokacin Da Ya Kama Hanyar Tafiya Afrika ta Kudu

Hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ICPC , ta bukaci duk ‘yan kasar da su dafawa shugaba Muhammadu Buhari a kokarin da yake na kakkabe cin hanci da rashawa a Najeriya.

Shugaban hukumar ICPC na shiyyar kudu maso yammacin Najeriya, Farfesa Olu Aina shine ya bukaci hakan alokacin da ya ziyarci gwamnan jihar Oyo Abiola Ajimobi a ofishin sa dake Ibadan. Farfesa Aina yace yaki da cin hanci da rashawa hakki ne da ya rataya kan dukkan mutanen Najeriya, maza da mata.

Shugaban hukumar ICPC din na shiyyar kudu maso yammacin Najeriya, yace sun kai yaki da cin hanci da rashawa har ga matasan wannan kasa, kana suna da cibiyoyin su a ko’ina a fadin kasar.

Shima gwamnan jihar Oyo Abiola Ajimobi, kira yayi ga ‘yan Najeriya da su canza halayensu marasa kyau zuwa masu kyau don kara gina kasa ta gari tare da samar da zaman lafiya, ya ci gaba da cewa a wannna lokacin ne ake bukatar canjin halaye da ‘dabi’un ‘yan Najeriya. Idan ba’a manta ba ya daura yaki da cin hanci da rashawa tun lokacin da ya dare karagar mulkin Najeriya.

Saurari Rahotan Hassan Tambuwal Daga Ibadan.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar ICPC Ta Bukaci ‘Yan Najeriya Su Goyi Bayan Buhari Don A Yaki Rashawa - 1'47"