Tawagar wadda ke dauke da kwamandan soji mai kula da kasashen Afirka janar David Rodriguez da kuma mataimakiyar sakatariyar tsaro ta kasar Amurka Amanda Doris, sun sami bayani daga shugaba Buhari wanda ya basu tabbacin cewar a watan Disamba ne ake sa ran za’a kammala yaki da ‘yan kungiyar Boko Haram, kuma a karya lagon su yadda ba zasuyi wani tasiri na tayar da zaune tsaye a Najeriya ba.
Akan haka ne wakilin Muryar Amurka Umar Farouk Musa, ya tuntubi wani soji kuma mai sharshi kan al’amurran tsaro a Najeriya, Janaral Abdurrazak Umar mai ritaya, domin jin tsokacinsa dangane da kokarin kammala yaki da Boko Haram a watan Disamba.
Sai dai Abdurrazak dai yace yaki ko karawa da ‘yan ta’adda ko ‘yan yakin sunkuru ba dai dai yake da yakin fito na fito ba, yaki da ‘yan ta’adda abu ne mai wahala domin su zasu mamayi mutane ne su shigo suyi barna, idan aka nemi a kara dasu sai su gudu. Ya kara da cewa yana da hatsari a fitar da lokaci guda ace za’a durkushe su, ba lalle bane a cimma buri ba.
Daga karshe janaral ya bayar da shawarar abinda yakamata ayi don samun galaba kan ‘yan bindigar masu tayar da kayar bayan, inda yace abu biyu za’ayi na farko shine a karfafa rudunonin sojoji da jami’an tsaro a fadin kasar, na biyu shine abu mafi muhimmamci wanda yake samun lagon su ko samun sirrunsu, ta hada bayanan sirri, kamar inda suke me suke shiryawa da makamantansu.