Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar IMF Ta Shawarci Najeriya Da Ta Karyar Da Darajar Naira


IMF Logo
IMF Logo

Hukumar bada lamani ta Duniya IMF ta shawarci gwamnatin Najeriya, data sake duba dokokin data kafa wanda ya shafi hada hadar kudaden kasashen waje, hakan ne ma yasa masana da yan kasuwa suka fara sharshi kan wannan shawara.

A sanarwar da wata jami’a a hukumar ta IMF mai suna Antoinette Sayer ta aikawa babban bankin Najeriya CBN, tace matakin na kawo cikas ga hada hadar kasuwancin cikin gida da na waje. Alhaji Kasimu Garba Kurfi shine shugaban kamfanin hada hadar kudi a saka jari na APT a birnin Lagos, wanda ya goyi bayan matakin da IMF din ta dauka, inda yace bayadda za’ayi ace Najeriya ta tsayar da farashin dala kasancewar bata da wadatar dalar.

Wakilin Muryar Amurka Babangida Jibrin, ya tambayi mukaddashin kungiyar masu hada hadar kudaden kasashen waje na Najeriya Alhaji Aminu Gwadabe, ko yaya masu hada hadar kudaden kasashen wajen ke kallon matakin gwamnati da kuma na IMF? Wanda ya bada amsa da cewa shi a ganin shi wannan shawarar bata dace ba, saboda IMF na tambayar Najeriya ne ta karyar da darajar Naira da cewa sai anyi haka ne kasar zata zama dai dai.

Ko a cikin wannan makon sai da gwamnan babban bankin tarayyar Najeriya, ya jaddada cewa gwamnati zata duba wannan tsari, domin tallafawa bankuna da kuma ‘yan kasuwa.

Saurari rahotan Babangida Jibrin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:51 0:00
Shiga Kai Tsaye

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG