Sama da million 2000 na cfa ne hukumar ta HALCIA tace ta yi nasarar karbowa daga hannun wadanda suka yi mursisi akan kudaden harajin fiton kaya da makamatansu.
A hirar shi da manema labarai, shugaban sashen kula da bincike a hukumar yaki da cin hanci Capitaine Sama’ila Elhadji Issouhou ya bayyana cewa, binciken ya shafi kudaden haraji da kuma wadansu kudaden da ba na haraji ba da ya kamata a sa a asusun gwamnati amma aka yi rubda ciki da shi.
Hukumar ta yabawa takwarorinta na wasu kasashen yammacin Afrika saboda gudunmuwar da suka bayar wajen gudanar da wannan bincike da ya shafi abubuwan da suka wakana a tsakanin shekarar 2018 zuwa 2020.
A nashi bayanin, kwamishina Ibrahim Alio Sanda ya ce kasashen da suke ba su hadin kai da goyon baya sun hada da Benin, Togo, da Burkinafaso,
Yanzu haka wasu jami’an hukumar HALCIA sun kaddamar da bincike ba sani ba sabo a wasu daga cikin ma’aiikatun ministoci a kalla 8 da nufin tantance wainar da aka toya a tsawon wasu shekaru a ci gaba da farafutar mahandama dukiyar kasa inji darektan yada labaranta Moutari Attaou.
Baya ga batun kwato kudade daga hannun masu kewayewa hanyoyin biyan haraji da hadin kan wasu baragurbin ma’aikata da wadanda ke karkata akalar dukiyar kasa, hukumar HALCIA ta sha alwashin ci gaba da bin diddigi don ganin an gurfanar da su a gaban koliya.
hukumar-halcia-mai-yaki-da-cin-hanci-a-nijer-ta-tashi-haikan-kan-batun-haraji
hukumar-yaki-da-cin-hanci-ta-nijer-ta-kudiri-aniyar-sa-ido-a-zaben-kasar
hukumar-yaki-da-cin-hanci-a-jamhuriyar-nijer-ta-kara-kaimi
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5