Tuni Fadar Shugaban Kasa ta tura sunan Bawa ga majalisar dattawa don tabbatar da shi.
Bawa kwararren mai binciken ne a kan Tattalin Arziki tare da kuma da kwarewa a fagen bincike, sannan kuma yana da kwarewa a fannin gabatar da kara da cin hanci da rashawa.
An sanar da shi a matsayin sabon shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa a cikin wani gajeren bayani daga fadar gwamnati a yau Talata.
Abdulrasheed Bawa dan shekara 40, ya fito daga karamar hukumar Jega ta jihar Kebbi, kuma ya jima yana aiki a matsayin jami’in EFCC.
Ya yi Makarantar Firamare a Birnin-kebbi, Sokoto inda ya sami shaidar makarantar firamare a 199. Ya kuma yi Makarantar Sakandaren Gwamnati, Owerri inda ya sami takardar shedar kammala makarantar sakandare a 1997. Sannan ya kammala a Jami'ar Usman Dan Fodio da ke Sokoto,
Babban jami’in leken asirin na daga cikin tsofaffin Jami’an EFCC Cadet Officers; kwas na daya, a shekarar 2005 kuma ya samu nasarar bincike tare da bayar da shaida a hari’u da dama da suka kai ga yanke hukunci da kuma dawo da bilyoyin naira da miliyoyin dalar Amurka daga duk fadin duniya.
A yanzu haka Mataimakin Babban Jami'in Tsaro ta DCDS ne tun shekarar 2016.
Karin bayani akan: EFCC, Abdurashid Bawa, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.