Hukumar CIA Ta Yarda Rasha Ta Yi Kutse a Zaben Amurka

Prime Ministan Rasha Vladiir Putin

Hukumar tattara bayanan sirri ta CIA a nan Amurka, ta amince cewa, Rasha ta yi kutse a zaben shugaban kasar da aka gudanar.

Jaridar ta wallafa labarin ne jiya Juma'a inda ta nuna cewa an yi kutsen da nufin taimakawa Donald Trump ya lashe ya zabe.

Jaridar ta ruwaito wata majiya da ba a bayyana sunanta ba, wadda ta tabbatar da maksudin yin kutsen.

Wannan labari na Washington Post na fitowa ne, bayan umurnin da shugaba Barack Obama ya bayar, na cewa a binciki zargin kutsen na Rasha.

Ina so na fayyace cewa, ba wai muna kalubalantar sakamakon zaben da aka yi ba ne, muna so ne mu yi abinda ya rataya a wuyanmu na kare mutuncin zabenmu.” Mataimakin kakakin sakataren yada labaran fadar White House Eric Schultz ya ce.

Yanzu haka an fara fuskantar matsin lamba daga bangaren ‘yan Democrat da na Republican a majalisar dokokin Amurka, inda suke kira da a yi cikakken bincike.