A cikin wasu rubuce-rubucen da ya sako akan danmdalinsa na Twitter ne Trump yake bayyana kudurinsa na bunkasa harakokin kasuwanci idan ya kama aiki gadan-gadan, amma ya kara da kasedin cewa duk kampanin dake zaton zai kori ma’aikatansa ko ya koma wata kasar waje, wai zai dawo ya rinka sayarda hajar tasa a nan Amurka ba tareda wasu matakan horo a kansa ba, to yana tapka kuskure ne kawai.
Haka kuma Trump, wanda zai dare kan shugabancin Amurka ran 20 ga watan Janaikrun sabuwar shekara, yace dimbin harajin tsallako kan iyakokin Amurka da kaya da zai dorawa kayan da ake sarrafawa a wasu kasashe, ana son a shigo da su zuwa cikin Amurka, zai kashe jikin duk masu tunanin irin wannan nau’i na kasuwanci.
Daga shekarar 2000 zuwa yau dai Amurka tayi asaran aiyukka sun kai milyan 5 a sanadin soma anfani da injuna masu anfani da komputoci da kuma kudurin wasu kampunna na tashi suna komawa kasashen ketare.