Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ta Hau Kujerar Naki A Kan Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Yakin Syria


Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin

Rasha tayi anfani da kujerar-na-kinta a zauren Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ko MDD a takaice, wajen toshe wani yunkurin da aka yi na samarda yarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon kwannaki 7 don a bada damar shiga da kayan agaji a cikin garin Aleppo dake kasar Syria, inda tarzomar da ake ta rutsa da dimbin mutanen garin.

Daga cikin kasashen dake kan Kwamitin, China ta goyi matsayin na Rasha, Venezuela ta ki goyon baya, yayinda Angola kuma ta tsabbace gefe guda, taki saka kowace irin kuri’a.

Da yake bayyana dalilinsu na daukar wannan matsayin, jakadan Rasha a MDD din, Vitaly Churkin yace a irin wannan lokacinda ake bayarwa na tsagaita wuta ne abokan gaba suke samun sararin kutsawa, su shigar da makamai da albarussai don karfafa gwiwar mayakan nasu, abinda yace kuma karshenta mutane fararen hula ne abin zai fi yi wa aibu.

Haka kuma jakadan na Rasha ya ce su kasashen da suka gabatarda bukatar a tsagaita wutar – Masar, New Zeland da Misra – duk Amurka da Faransa ne ke ingiza su.

XS
SM
MD
LG