Yayin da ake kokarin ceto 'yan matan makarantar Chibok da 'yan kungiyar Boko Haram ke rike dasu yau fiye da wata guda hukumar bada agajin gaggawa ko NEMA a takaice ta kai tallafin kayan abinci garin na Chibok
WASHINGTON, DC —
Hukumar Bada Agajin Gaggawa ko NEMA a takaice ta kai tallafin kayan abinci a garin Chibok, garin da kungiyar Boko Haram ta sace 'yan matan makarantar sakandare fiye da 276.
Al'ummar yankin Chibok din suna fama da matsalar karancin abinci domin shiga yankin nada wuya sakamakon matsalar tsaro da ake fama da ita. Alhaji Muhammed Kanal babban jami'in hukumar ta NEMA mai kula da yankin arewa maso gabas ya bayyana halin da al'ummar Chibok ke ciki. Yace uanzu garin Chibok mota bata zuwa, mutane basa zuwa. Abinci baya zuwa sabili da ahaka sai aka soma karancin abinci a garin da kewaye. Yace dalili ke nan hukumar ta dauki dimbin abinci zuwa garin inda ana ta rabawa tun daga safe har yamma da fatan Allah ya dawo da yaran lafiya.
Kamar Chibok a jihar Adamawa ma akwai dubban 'yan gudun hijira da kungiyar Boko Haram ta tilasta masu barin muhallansu daga yankin jihar Borno dake makwaftaka da Adamawa domin su tsira da rayukansu. A nan jihar ma NEMA ta kai tallafi kamar yadda Alhaji Haman Haruna Foro babban sakataren hukumar ta jihar Adamawa ya bayyana. Ya godewa garuruwan da suka karbi 'yan gudun hijirar lamarin da yace ya taimakesu da aikinsu.
Akwai bukatu da yawa. Suna bukatar magunguna. Suna bukatar gidan sauro domin yanzu sauro zai yi yawa domin lokacinsa ne. Akwai gidajen shan magani na jihar to yanzu ya zama wajibi a cikasu da magunguna domin karuwar mutane. Akwai kuma karancin wurin bayan gida. Dole a kara. Yakamata kuma akara ruwa domin mutanen sun fi karfin tanadin da gwamnatin jihar ta yiwa ainihin mutanen wurin.

Your browser doesn’t support HTML5