Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Jonathan Ya Soke Zuwa Chibok, Ya Doshi Faransa


Shugaba Francois Hollande na Faransa da Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya.
Shugaba Francois Hollande na Faransa da Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya.

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya soke shirin zuwa garin Chibok.

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya soke shirin zuwa garin Chibok, inda ‘yan Boko Haram suka saci dalibai mata ‘yan makaranta su fiye da 200 a watan da ya shige.

Jami’ai sun fada a yau jumma’a cewa Mr. Jonathan ya kasa zuwa Chibok dake Jihar Borno a saboda dalilai na tsaro.

A yanzu shugaban na Najeriya zai wuce zuwa Paris a Faransa domin wani taron kasashe makwabtan Najeriya da shugaba Francoise Hollande ya kira. Su ma shugabannin kasashen Benin, Kamaru, Nijar da Chadi zasu halarci taron.

A nan Washington, darekta mai kula da harkokin Afirka a ma’aikatar tsaron Amurka, Alice Friend, ta fadawa wani kwamitin majalisar dattijai cewa Najeriya ba ta da suna mai kyau kan batun yaki da Boko Haram.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG