Zanga-zangar wanda ta kasance ta lumana an gudanar da ita ne karkashen inuwar zauren gamayya na kungiyoyin sa kai da na kwararru da kuma dalibai dake jihar kano.
Hajiya Amina Hanga, daya daga cikin wadanda suka shirya gangamin tace”mun zo ne domin mu nuna cewa mundamu akan bacewar ‘yan matan nan,mu nunawa iyaye da sauran jama’a kada suga cewa kamar su kadai ne akwai mutane da suka damu shi yasa muka taru anan yau.”
Kungiyar mata lauyoyi ta Najeriya,na daga cikin kungiyoyin da suka shiga cikin wannan gangami, Barister Huwaila Ibrahim Muhammad sakataren kungiyar na mai cewa “burin da muke son cimma shine muyi kokari muga hanyoyin da za’a bunkasa tsaro a kasarmu, kuma wannan abunda ya faru kada ya kara faruwa,kuma muna son mu saka masawa gwamnati da ayi kokari duk halin yanda za’a yi a fito mana da yaran mu lafiya kamar yanda aka dauke su."
Gangamin ya kunshi iyaye da ‘yan m,ata matasa ‘yan asalin yankin Chibok masauna Kano kamar Fatima Askira inda tace “gaskiya wannan abun karya zuciya ne kuma abun bakin ciki ga duk wata mace ko na miji,wadannan yaran mata ne kullum kuka mukeyi akan su dawo bai kamata ace an bar yaran nan fiye da wata daya a hannun irin wadannan mugaye ba komai na iya samun su,idan dai sibiliyan zasu iya kaiwa ‘yan boko haram hari ban ga dalilin da yasa gwamnati zata dauki abun da wasabi,bayan sun san inda suke a fadan su.