Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duk da Matsalar Boko Haram Najeriya Nada Tagomashi a Duniya


Shugaban Najeriya da wasu shugabannin duniya.
Shugaban Najeriya da wasu shugabannin duniya.

Gwamnatin Najeriya tace tana samun karbuwa a kasashen duniya duk da rikicin da Boko Haram ke haddasawa a kasar

Najeriya ta yi ikirarin dada samun karbuwa daga kasashen duniya duk da rikicin da kungiyar Boko Haram ke haddasawa cikin kasar.

Bisa ga alamu rikicin da ya addabi kasar bai shafi tagomashin da take da shi ba a idanun duniya.Ministan Kasa a Ma'aikatar Ayyuka kuma mai kula da Ma'aikatar Tsare-tsare Ambasada Bashir Yuguda yace taron cigaban tattalin arzikin duniya akan nahiyar Afirka da aka gudanar a kasar ya nuna har yanzu Najeriya nada tasiri akan idanun duniya.

Ambasada Bashir Yuguda yace duk da matsalar tsaron da kasar ke fuskanta bai hana baki zuwa kasar ba domin su tattauna akan tattalin arziki. Kasashen duniya sun yadda su zo Najeriya su taru. Bayan haka sun tausayawa kasar kuma sun kuduri aniyar taimakawa domin a kawo karshen ta'adancin kungiyar Boko Haram da ma ta'adanci gaba daya.

Ministan yayi jawabinsa ne a wani taron da aka shiryawa daraktocin ma'aikatar tsare-tsare da aka yi a Minna babban birnin jihar Neja.

A nashi jawabin gwamnan jihar Neja Dr Muazu Babangida Aliyu yace alatilas dole gwamnatin tarayya ta fatartaki 'yan kungiyar Boko Haram nan da watanni uku masu zuwa idan ana bukatar cigaban tattalin arzikin kasar. Yace yanzu lokaci yayi na yakar 'yan kungiyar gadan gadan. Yace "ya kamata mu yakesu har sai mun kai ga cin nasara. Bai kamata mu kyale har a ce za'a je ana shawara dasu ba, a'a"

Shi kuma shugaban Izala a Najerya Sheikh Abdullahi Bala Lau yace shigo da sojojin waje su yaki kungiyar Boko Haram ba nan kadai gizo ke saka ba. Yace bature ba zai iya fitar da kasar daga halin da ta shiga ba. 'Yan Najeriya ne da kansu zasu iya yin hakan.Idan turawa sun zo sun tafi wanene zai cigaba da kula da kasar. Yace matsalar 'yan Njeriya ce. Su suka san abubuwan da suke yi su ne kuma suka san inda kansu ke ciwo. Domin haka 'yan Najeriya yakamata su hadu su tattauna su koma su nemi mafita.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG