Hukumar Alhazan Najeriya NAHCON Ta Ce Maniyyata Su Tanadi Naira Miliyan 4.5

Hukumar Alhazan Najeriya NAHCON lokacin taron batun Hajjin 2024

A shirye-shirye ta na gudanar da aikin Hajjin shekarar 2024, hukumar Alhazai ta Najeriya, NAHCON ta bukaci maniyyata da su ajiye Naira miliyan 4.5 a matsayin kudin ajiya mafi karaci a asusun su na tafiya domin su biya kudin kujera idan lokaci ya yi. 

ABUJA, NIGERIA - Hukumar ta ce ta yi la'akari ne da yanayin canjin kudi daga Naira zuwa Dalar Amurka wanda yake Naira 714 kan dala daya a yanzu. Shugaban hukumar Zikirullahi Kunle Hassan ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.

Hukumar Alhazan Najeriya NAHCON lokacin taron batun Hajjin 2024

Zikirullahi ya ce akwai alamun cewa aikin hajjin badi zai yi tsada, saboda haka hukumar ta fara taro da hukumomin kula da aikin hajji na jihohi da kungiyar masu jiragen jigilar Alhazai domin yin bitar rahoton aikin hajjin wannan shekara.

Zikirullahi ya ce duk da tsaiko da hukumar ta samu sakamakon rikicin Sudan, a karon farko cikin shekaru 10, hukumar ta kwashe Alhazan ta dubu 95 a ciki da wajen Saudiyya lami lafiya.

Ya ce dole ne hukumar ta fara shirye-shirye tun yanzu domin babu tabbas na yadda al'amura za su kasance nan da wasu wattani masu zuwa.

Shi ma Kwamishinan kula da sashen gudanarwa na hukumar Alhazai Abdullahi Magaji Hardawa ya ba da hujojjin daukar wannan mataki na bai wa maniyata shawara kan kudin kujerar aikin hajji.

Hukumar Alhazan Najeriya NAHCON lokacin taron batun Hajjin 2024

Hardawa ya ce wannan shawara ce mai ma'ana domin sama da kashi 97 cikin 100 na harkar kudin aikin Hajji a Najeriya akan canja shi ne daga Naira zuwa Dalar Amurka, shi ya sa aka ba da shawara ga duk wani maniyyaci da ke sha'awar zuwa hajji a shekara mai zuwa ya ajiye kudi wanda ba zai gaza Naira Miliyan hudu da rabi ba.

Hardawa ya ce "idan an ayyana kudin Hajji, idan har kudin kujera bai kai haka ba, za'a mayar wa maniyyaci da sauran kudin sa, in kuma ya fi haka, sai a gaya masa ya yi ciko.

Alhaji Laminu Rabi'u ‘Dan Bappah daraktan hukumar aikin Hajji na jihar Kano, ya ce wannan lamari sai addu'a, domin wannan tsada ta kai gaya, fata kawai shi ne Allah ya yaye wa dukan maniyyaci, ya ba shi ikon zuwa.

Hukumar Alhazan Najeriya NAHCON lokacin taron batun Hajjin 2024

Amma ga mai nazari kan al'amuran yau da kullum, Abubakar Aliyu Umar, ya kamata hukumar Alhazai ta dauki wasu matakai na kulawa da alhazai sosai idan har sun biya irin wannan kudade masu yawa.

Hukumar ta raba kujeru ga jihohin kasar inda jihar Kaduna ta samu kujeru mafi yawa da 6004, sai JIhar Kano da 5,934, jihar Sokoto ta samu 4,996 sai jihar Kebbi da 4.752. Jihohin Abia da Akwa ibom ba su samu kujeru ba har kawo yanzu.

Saurari ciakken rahoto daga Medina Dauda:

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Alhazan Najeriya NAHCON Ta Ce Maniyyata Su Tanadi Naira Miliyan 4.5