Wannn na faruwa a shekara ta biyu da Saudiyya ta dakatar da damar maniyatan ketare daga shiga kasar don aikin hajjin sanadiyyar annobar coronavirus.
A sanarwar daga jami'ar labarun hukumar Fatima Sanda Usara ta fitar, ta ce kamfanonin na nuna cewa da izinin NAHCON su ke bugun kirjin za su kai mutane aikin hajjin da VISA ta shiga Saudiyya ba ta aikin hajji ba.
NAHCON ta bukaci jama'a su yi takatsantsan da irin wadannan kamfanoni da ta kwatanta a matsayin masu karambani.
Mun tambayi daya daga cikin masu kamfanonin alhazan Auwal Lalla kan irin wadannan dillalai masu zamba cikin aminci, ya ce lallai ko da an samu kamfanonin, to aikin baban giwa kawai suke yi.
Karin bayani akan: hajjin, hajji, NAHCON, Saudiyya, VISA, Fatima Sanda Usara, Nigeria, da Najeriya.
Hukumar alhazai ta bukaci maniyyata su kwantar da hankali da jiran har al'amura su daidaita don bude zuwa hajjin, haka nan da amfani da hanyar adashen kudin hajji na hukumar musamman ga maniyyata masu karamin karfi.
A yayin da ake shirin hawa Arfa ranar 19 ga watan nan na Yuli, Saudiyya ta fara cafke masu yunkurin shiga wajajen aikin hajji ba da izini ba da cin tarar su riyal dubu 10 wato fiye da Naira miliyan daya kenan.
Saurari rahoto cikin sauti daga Nasiru Adamu El-hikaya:
Your browser doesn’t support HTML5
Hukumomin Saudiyya Sun Shirya Karban Alhazai a Mina
Your browser doesn’t support HTML5