Hukumar Kwastan Tayi Babban Kamu

Jami'an kwastan din Hong Kong ranar Talatan nan sun cafke hakoran giwa da nauyinsu ya kai kilo 1,120 da hakoran mugun dawa 13 da fatun damisa 5 dukansu nauyinsu ya kai kilo 2,266 a cikin wani akwati duk daga Najeriya zuwa kasar Hong Kong.

Hukumar kwastan shiya ta daya dake kula da jihohin yammacin Najeriya ta kama kayan fiye da Naira Miliyan dari daga hannun ‘yan fasa kwauri.

Shugaban shiyar Sani madugu ya shaidawa manema labarai a birnin Ikko cewa, matakin ya biyo bayan rahotanni ne da hukumar ke samu daga ‘yan kasa dake tsegunta mata abubuwan dake faruwa a kan iyakokin Najeriya.

Shugaban hukumar kwastan din na shiyar yace kayayyakin da hukumar ta kama, kayayyaki ne da gwamnatin tarayya ta haramta shigo da su da suka hada da yankakkun kaji da talotalo da aka daskara da kankara. Banda haka kuma yace hukumar ta kama miyagun kwayoyi duk da yake akwai hukumar dake sa ido kan safarar miyagun kwayoyi a Najeriya.

Ya bayyana cewa, hukumar ta sami nasarori da dama. Bisa ga cewarsa, duk da yake gwamnati bata haramta shigo da shinkafa ba, sun kama mutanen da suke kokarin komawa su shigo da ita ta bayan fage ba tar da biyan haraji ba. Yace sun sami buhunnan shinkafa fiye da dubu goma da ake kokarin shigowa da su ta barauniyar hanya.

Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Babangida Jibril ya aiko mana daga birnin Ikko.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Kwastan tayi babban kamu-3"23