Hukumar hada-hadar kasuwanci ta jiragen ruwa zata kammala gina tasoshin tudu a jihohin da basa gabar teku nan da shekara daya.
A tasoshin ne za'a dinga sauke kaya. Tasoshin zasu zama cibiyar sauke kaya inda za'a dinga kasuwanci maimakon dan kasuwa ya je Legas domin dauko kaya.
Za'a dinga jigilar kayan ta manyan motoci da jiragen kasa kamar yadda zamanin mulkin malka turawa ke hada-hadar auduga da fatu da gyada daga lardin arewa.
Alhaji Hassan Bello babban sakataren hukumar ya kara yin bayani. Yace yanzu ma ana kai kayan ana ajiyewa a Kaduna. Kullum tarago na zuwa daga Legas. A nan mutum zai biya kudin kwastan akan kayan da ya shigo dasu daga waje.Idan kuma za'a aika kaya waje sai a yi a tashar Kaduna.
Irin tashar za'a gina a Oyo da Funtua da Jos da Kano da kuma Maiduguri. Tasoshin zasu habaka tattalin arziki.Nufin shi ne koina kasar a samu habaka harkokin kasuwanci. Sabda haka jihohi da yawa sun nemi a sakasu cikin shirin.
Shi ma gwamnan jihar Filato ya je ofishin hukumar yana neman lallai a gina tashar a jiharsa saboda an samu zaman lafiya yanzu.
Jami'ar hukumar Rabi Sulu Gambari na ganin jihohin kan iyakokin Najeriya da kasashen Chadi, Nijar da Kamaru zasu ci gajiyar shirin domin mutanen yankin nada halin kaza da ta kwana kan dami
Ga karin bayani.